2 Thessalonians 1

1Wasiƙa daga Bulus, da Sila, da Timoti,

zuwa ga ikkilisiya ta Tassalonikawa ta Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi:

2Alheri da salama zuwa gare ku daga Allah Uba da kuma Ubangiji Yesu Kiristi.

Godiya da Adduʼa

3Dole kullum mu gode wa Allah saboda ku, ʼyanʼuwa, haka kuwa ya dace, domin bangaskiyarku tana girma gaba gaba, ƙaunar da kowannenku yake yi wa juna kuwa tana ƙaruwa. 4Saboda haka, a cikin ikkilisiyoyin Allah muna taƙama game da ɗaurewarku da kuma bangaskiyarku cikin dukan tsanani da gwaje-gwajen da kuke sha.

5Dukan wannan yana tabbatar cewa hukuncin Allah daidai ne, saboda haka kuma za a lissafta ku a kan kun cancanci mulkin Allah, wanda dominsa ne kuke shan wahala. 6Allah mai adalci ne: Zai sāka wa masu ba ku wahala da wahala 7yǎ kuma sauƙaƙa muku ku da kuke wahala, har ma da mu. Wannan zai faru saʼad da aka bayyana Ubangiji Yesu daga sama cikin wuta mai ci tare da malaʼikunsa masu iko. 8Zai hukunta waɗanda ba su san Allah ba da kuma waɗanda ba su yi biyayya da bisharar Ubangijinmu Yesu ba. 9Za a hukunta su da madawwamiyar hallaka a kuma kau da su daga gaban Ubangiji da kuma daga ɗaukakar ikonsa 10a ranar da zai dawo don a ɗaukaka shi a cikin mutanensa masu tsarki, yǎ kuma zama abin banmamaki ga dukan waɗanda suka gaskata. Wannan ya haɗa har da ku, domin kun gaskata shaidar da muka yi muku.

11Sane da wannan, kullum muna adduʼa saboda ku, don Allahnmu yǎ sa ku cancanci kiransa, ta wurin ikonsa kuma yǎ cika kowace manufarku mai kyau da kuma kowane aikin da bangaskiyarku ta iza. 12Muna wannan adduʼa don sunan Ubangijinmu Yesu yǎ sami ɗaukaka a cikinku, ku kuma a cikinsa, bisa ga alherin Allahnmu da na Ubangiji Yesu Kiristi.
Ko kuwa Allah da Ubangiji, Yesu Kiristi


Copyright information for HauSRK